(ABNA24.com) M. Aoun, ya ce kalamman da jakadiyar Amurka a Beirut, ta firta a baya baya nan tsoma baki ne dumu dumu a harkokin cikin gidan kasar ta Labanon, kamar yadda ya fada a wata hira ta musamman da gidan talabijin na harshen Larabci na al-Mayadeen.
Amurkawa suna tsoma baki kai tsaye cikin harkokin cikin gidan na Lebanon, kuma wannan ba abu ne da ba za a yarda da shi ba, inji shugaban kasar ta Labanon.
Ita dai jakadiyar Amurka a Labanon, ta soki kungiyar Hezbollah, wanda kuma lamarin bai yi wa ‘yan kasar ta Labanon dai ba ko kadan.
Shugaba Aoun, ya jaddawa Amurka cewa, kungiyar Hezbollah tana wakiltar al'ummar Lebanon ne kuma tana da farin jini a tsakanin mutane, wanda kuma irin wadanan kalamman na suka da jakadiyar Amurka ta yi tsoma baki ne kai tsaye cikin harkokin gidan kasar ta Labanon.
Dama kafin hakan, tun da farko a ranar, Ministan Harkokin Wajen Lebanon, Nassif Hitti, ya kirayi jakadiyar ta Amurka a kasar, Dorothy Shea, domin bayyana mata bacin ran kasar kan sukar da ta yi wa kungiyar ta Hezbollah.
/129
29 Yuni 2020 - 07:03
Lambar labari: 1051189
Shugaban Labanon, Michel Aoun, ya yi tir da katsalandan din da Amurka ke yi a cikin harkokin cikin gidan kasar,.